Mark 12:25 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da matattu suka tashi, ba za su yi aure ba, ba kuwa za a ba da su ga aure ba. Za su zama kamar yadda mala’iku suke a cikin sama.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
لُواْكَثِنْ دَ مَتَتُّو ذَاسُ تَاشِ، مَظَا بَذَاسُيِ عَوْرٜىٰ بَ، مَتَ كُمَ بَذَاعَ بَادَسُو غَ عَوْرٜىٰبَ، عَمَّا ذَاسُ ذَمَ كَمَرْ مَلاَىِٕكُنْ دَسُكٜىٰ ثِكِنْ سَمَنٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Domin in an tashi daga matattu, ba a aure, ba a aurarwa, amma kamar mala'ikun da suke Sama ake.