Mark 12:36 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dawuda da kansa ya yi magana ta wurin Ruhu Mai Tsarki ya ce, “ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a hannun damana sai na sa abokan gābanka a ƙarƙashin sawunka.” ’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَاوُدَ دَ كَنْسَ، تَوُرِنْ إِيكُوانْ رُوحُ مَيْ ڟَرْكِے يَثٜىٰ، « ‹ عُبَنْغِجِ يَثٜىٰ وَ عُبَنْغِجِنَ ، ذَوْنَ أَ حَنُّنْ دَامَنَ، سَيْنَا سَا أَبُواْكَنْ غَابَنْكَ عَڧَرْڧَشِنْ ڧَڢَاڢُنْكَ؞› »
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Domin Dawuda kansa, ta ikon Ruhu Mai Tsarki ya ce, ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina, Zauna a damana, Sai na ɗora ka a kan maƙiyanka.’