Mark 13:1 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da yake barin haikalin, sai ɗaya daga cikin almajiransa ya ce masa, “Malam! Dubi irin manya-manyan duwatsun nan! Ka ga irin gine-ginen nan masu kyau mana!”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عِيسَىٰ يَنَ ڢِتُواْوَ كٜىٰنَنْ دَغَ هَيْكَلِ، سَيْ طَيَ دَغَ ثِكِنْ أَلْمَجِرَنْسَ يَثٜىٰ مَسَ «مَلَمْ، دُوبِے مَنْيَنْ دُووَڟُنَّنْ دَ غِنٜىٰ غِنٜىٰنَّنْ مَاسُ بَنْ مَامَاكِ!»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yesu na fita daga Haikalin, sai ɗaya daga cikin almajiransa ya ce masa, “Malam, dubi irin duwatsun nan da gine-ginen nan!”