Mark 14:32 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Suka tafi wani wurin da ake kira Getsemane, Yesu ya kuma ce wa almajiransa, “Ku zauna a nan, yayinda ni kuwa in yi addu’a.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سُكَ تَڢِے وَنِ وُرِنْ دَ عَكٜىٰ ثٜىٰ دَشِ غٜىٰڟٜىٰمَنِ وَتُواْ، وُرِنْ مَڟٜىٰوَرْ یَیَنْ ظَيْتُنْ، سَيْ عِيسَىٰ يَثٜىٰ وَ أَلْمَجِرَنْسَ «كُذَوْنَ أَنَنْ؞ ذَنْجٜىٰ إِنْيِ أَدُّعَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai suka isa wani wuri, wai shi Getsamani. Ya ce wa almajiransa, “Ku zauna nan har in yi addu'a.”