Mark 14:43 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yana cikin magana ke nan, sai Yahuda, ɗaya daga cikin Sha Biyun ya bayyana. Ya zo tare da taro da suke riƙe da takuba da sanduna. Manyan firistoci da malaman dokoki, da kuma dattawa ne suka turo taron.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عِيسَىٰ يَنَ ثِكِنْ مَغَنَ كٜىٰنَنْ، سَيْغَا يَهُودَ، طَيَ دَغَ ثِكِنْ أَلْمَجِرَنْسَ شَا بِيُنَّنْ، يَا ذُواْ تَرٜىٰدَ مُتَنٜىٰ دَيَوَ سُنَ رِڧٜىٰ دَ تَكُبَ دَ سَنْدُنَ؞ مَنْيَنْ ڢِرِسْتُواْثِے دَ مَلَمً كُواْيَرْوَرْ مُوسَٰى دَ شُوغَبَنِّ نٜىٰ سُكَ تُرُواْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Nan da nan, kafin ya rufe baki sai ga Yahuza, ɗaya daga cikin sha biyun nan, da taron mutane riƙe da takuba da kulake, manyan firistoci, da malaman Attaura, da shugabanni ne suka turosu.