Mark 14:61 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma Yesu ya yi shiru, bai kuwa amsa ba. Babban firist ya sāke tambayarsa ya ce, “Kai ne Kiristi, Ɗan Mai Albarka?”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا عِيسَىٰ يَيِ شِضُ، بَيْبَاشِ كُواْ أَمْسَبَ؞ سَيْ بَبَّنْ ڢِرِسْتِ طِنْ يَسَاكٜىٰ تَمْبَيَرْسَ «كُواْ كَيْنٜىٰ أَلْمَسِيحُ طَنْ مَيْ أَلْبَرْكَ؟»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma yana shiru abinsa, bai amsa kome ba. Sai babban firist ɗin ya sāke tambayarsa, “To, ashe, kai ɗin nan ne Almasihu Ɗan Maɗaukaki?”