Mark 15:1 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da sassafe, sai manyan firistoci da dattawa, da malaman dokoki, da dukan Majalisa, suka yanke shawara. Suka daure Yesu, suka kai shi, suka miƙa shi ga Bilatus.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَ سَسَّڢٜىٰ مَنْيَنْ ڢِرِسْتُواْثِے دَ شُوغَبَنِّ دَ مَلَمً كُواْيَرْوَرْ مُوسَٰى دَ دُكَنْ سَوْرَنْ یَنْ مَجَلِسَ سُكَيِ شَوَرَا؞ سَيْ سُكَ طَوْرٜىٰ عِيسَىٰ ، سُكَ تَڢِے دَشِ، غَبَنْ بِلَتُسْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da wayewar gari sai manyan firistoci da shugabanni, da malaman Attaura, da dukkan 'yan majalisa suka yi shawara. Sai suka ɗaure Yesu, suka tafi da shi, suka ba da shi ga Bilatus.