Mark 2:14 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yana cikin tafiya, sai ya ga Lawi, ɗan Alfayus zaune a inda ake karɓar haraji. Yesu ya ce masa, “Bi ni.” Sai Lawi ya tashi, ya bi shi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَنَ وُثٜىٰوَ سَيْ يَغَ لَوِ طَنْ هَلْڢَ يَنَ ظَوْنٜىٰ أَوُرِنْ كَرْٻَرْ هَرَاجِ؞ سَيْ عِيسَىٰ يَثٜىٰ مَسَ «بِينِ؞» سَيْ يَتَاشِ يَبِے شِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yana cikin wucewa, sai ya ga Lawi ɗan Halfa a zaune yana aiki a wurin karɓar haraji. Yesu ya ce masa, “Bi ni.” Sai ya tashi ya bi shi.