Mark 2:21 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Ba mai facin sabon ƙyalle a tsohuwar riga. In ya yi haka, sabon ƙyallen zai yage daga tsohuwar, yagewar kuwa za tă zama da muni.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«بَا مَيْ ڢَاثِنْ ڟُواْهُوَرْ رِغَا دَ سَابُوانْ يَدِ؞ عِدَنْ كُوَ يَيِ، سَيْ سَابُوانْ يَدِنْ يَنَطٜىٰ ڟُواْهُوَرْ رِغَرْ، حَرْ يَاغٜىٰوَرْ تَڢِے تَدَا مُونِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ba mai mahon tsohuwar tufa da sabon ƙyalle. In ma an yi, ai, sai sabon ƙyallen ya kece tsohuwar tufar, har ma ta fi dā kecewa.