Mark 2:22 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ba wanda yakan zuba sabon ruwan inabi a tsofaffin salkuna. In ya yi haka, ruwan inabin zai farfashe salkunan, yă yi hasarar ruwan inabin, salkunan kuma su lalace. A’a, yakan zuba sabon ruwan inabin a sababbin salkuna.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كُمَ بَاوَنْدَ ذَيْظُبَا سَابُوانْ ضُوً إِنَبِے عَثِكِنْ ڟُواْڢَڢِّنْ سَلْكُنَ؞ عِدَنْ يَا يِهَكَ، سَيْ ضُوً إِنَبِنْ يَڢَرْڢَشٜىٰ سَلْكُنَنْ، عَكُمَيِ هَسَرَرْ سَلْكُنَنْ دُكْ دَ ضُوً إِنَبِنْ؞ أَيْ، سَابُوانْ ضُوً إِنَبِے، سَيْ سَابَبِّنْ سَلْكُنَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ba kuma mai ɗura sabon ruwan inabi a tsofaffin salkuna. In ma an ɗura, sai ruwan inabin ya fasa salkunan, a kuma yi hasara tasa da ta salkunan. Sabon ruwan inabi, ai sai sababbin salkuna.”