Mark 4:20 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Waɗansu mutane kuwa suna kama da irin da aka shuka a ƙasa mai kyau, sukan ji maganar Allah, su kuma karɓa, sa’an nan kuma su fid da amfani riɓi talatin-talatin, ko sittin-sittin, ko ɗari-ɗari.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
إِرِنْدَ يَڢَاطِ أَوُرِنْ دَ يَكٜىٰدَ ݣَوْ كُوَ، شِينٜىٰ ݣُوتَنْثِنْ وَطَنْدَ سُكَجِ كَلْمَرْ اللَّهْ ، سُكَ كَرْٻَ، سُكَ كُمَيِ أَمْڢَانِ دَ عِتَ، حَرْ سُكَيِ رِيبَ وَطَنْسُ تَلَاتِنْ تَلَاتِنْ، وَطَنْسُ سِتِّنْ سِتِّنْ، وَطَنْسُ مَا حَرْ طَرِے طَرِے؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Waɗanda aka shuka a ƙasa mai kyau kuwa, su ne kwatancin waɗanda suke jin Maganar, su karɓa, su kuma amfana, waɗansu riɓi talatin talatin, waɗansu sittin sittin, waɗansu ma har ɗari ɗari.”