Mark 6:31 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
To, saboda mutane da yawa suna kai da kawowa, har ma ba su sami damar cin abinci ba, sai ya ce musu, “Ku zo mu kaɗaita inda ba kowa don ku ɗan huta.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَاشِ كُوَ مُتَنٜىٰ دَيَوَ سُنَ تَكَيْوَ دَ كَٰوُاْوَ، حَرْ مَنْذَنِّےنْ بَسُ سَامِ دَامَرْ ثِنْ عَبِنْثِبَ، سَيْيَثٜىٰ مُسُ «كُذُواْ مُتَڢِے وُرِنْ دَ بَا كُواْوَ، دُوانْ كُطَنْ هُوتَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya ce musu, “Ku zo mu kaɗaita a wurin da ba kowa, ku ɗan huta.” Domin mutane da yawa suna kaiwa suna kawowa, ko damar cin abinci ma, manzannin ba su samu ba.