Mark 9:13 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma ina faɗa muku, Iliya ya riga ya zo, kuma suka yi duk abin da suka ga dama da shi, kamar yadda aka rubuta game da shi.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَيْ، إِلْيَاسُ يَا رِغَا يَاذُواْ، مُتَنٜىٰ سُكَ كُمَيِ مَسَ دُكْ أَبِنْدَ سُكَغَ دَامَ، كَمَرْ دَيْ يَدَّ عَكَ رُبُوتَ ذَيْ ڢَرُ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma ina gaya muku, Iliya ya riga ya zo, sun kuma yi masa abin da suka ga dama, yadda labarinsa yake a rubuce.”