Mark 9:2 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Bayan kwana shida, sai Yesu ya ɗauki Bitrus, Yaƙub da Yohanna tare da shi, ya kai su kan wani dutse mai tsawo, suka kasance su kaɗai a wurin. A can aka sāke kamanninsa a gabansu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَايَنْ ݣُونَ شِدَ عِيسَىٰ يَطَوْكِ بِتْرُسْ دَ يَعْڧُوبَ دَ يَحْيَى، يَكَيْسُ كَنْ وَنِ بَبَّنْ تُدُ مَيْ ڟَوُاْ عِنْدَ سُكَ كَسَنْثٜىٰ سُو كَطَيْ؞ أَنَانً سَيْ كَمَنِّنْسَ يَثَنْجَ أَغَبَنْسُ،
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Bayan kwana shida Yesu ya ɗauki Bitrus, da Yakubu, da Yahaya, ya kai su kan wani dutse mai tsawo, su kaɗai. Sai kamanninsa ya sāke a gabansu,