Matthew 1:17 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ta haka akwai zuriya goma sha huɗu ke nan duka-duka daga lokacin Ibrahim zuwa lokacin Dawuda, goma sha huɗu kuma daga Dawuda zuwa bauta a Babilon, goma sha huɗu kuma daga bauta a Babilon zuwa Kiristi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَتُواْ دُكَنْ ڟَارَا دَغَ إِبْرَٰهِيمْ ذُوَا دَاوُدَ، ڟَارَا غُواْمَشَا حُطُ ثٜىٰ؞ دَغَ دَاوُدَ ذُوَا لُواْكَثِنْ دَ عَكَ ݣُوشِ إِسْرَٰٓءِيلَاوَا ذُوَا بَوْتَا عَ بَابِيلَ، ڟَارَا غُواْمَشَا حُطُ ثٜىٰ دَغَ بَوْتَا عَ بَابِيلَ كُمَ ذُوَا حَيْڢُوَرْ أَلْمَسِيحُ ، ڟَارَا غُواْمَشَا حُطُ ثٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Wato, dukkan zuriya daga Ibrahim zuwa kan Dawuda, zuriya goma sha huɗu ce. Daga Dawuda zuwa ga ɗebe su a kai Babila kuwa, zuriya goma sha huɗu. Daga ɗebe su zuwa Babila zuwa kan Almasihu, zuriya goma sha huɗu.