Matthew 12:45 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai yă je yă ɗebo waɗansu ruhohi bakwai da suka fi shi mugunta, su kuwa zo su shiga su zauna a can. Ƙarshen mutumin nan fa zai fi farkonsa muni. Haka zai zama ga wannan mugun zamani.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ يَكُواْمَ يَݣُوسُواْ وَطَنْسُ ڧَظَامَنْ رُوحُواْحِ غُدَا بَݣَويْ، وَطَنْدَ سُكَڢِيشِ مُغُنْتَا، سُذُواْ سُشِغَ سُذَوْنَ أَوُرِنْ؞ عَڧَرْشٜىٰ، ذَمَنْ مُتُمِنَّنْ ذَيْڢِ نَڢَرْكُوانْ مُونِ؞ حَكَ مَا ذَيْ ذَمَ غَ مُتَنٜىٰنْ وَنَّنْ زَامَانِ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Daga nan ya je ya ɗebo waɗansu aljannu bakwai da suka fi shi mugunta. Sai su shiga su zauna a wurin. Wannan mutum ƙarshen zamansa ya fi na fari lalacewa. Haka zai zamar wa wannan mugun zamani.”