Matthew 14:13 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da Yesu ya ji abin da ya faru, sai ya shiga jirgin ruwa ya janye shi kaɗai zuwa wani wuri inda ba kowa. Da jin haka, taron mutane suka bi shi da ƙafa daga garuruwa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَ عِيسَىٰ يَجِ حَكَ، سَيْ يَتَاشِ يَشِغَ جِضْغٍ ضُوَ يَهَيٜىٰ ذُوَا وَنِ وُرِے عِنْدَ بَا كُواْوَ دُواْمِنْ يَكَسَنْثٜىٰ شِ كَطَيْ؞ عَمَّا دَ تَارُوانْ مُتَنٜىٰنْ سُكَجِ حَكَ، سَيْ سُكَ ڢِتُواْ دَغَ غَرُرُوَ سُكَبِيشِ دَ ڧَڢَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da Yesu ya ji haka sai ya tashi daga nan, ya shiga jirgi zuwa wani wuri inda ba kowa, domin ya kaɗaita. Amma da taron jama'a suka ji haka, suka fito daga garuruwa suka bi shi da ƙafa.