Matthew 15:22 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Wata mutuniyar Kan’ana daga wajajen ta zo wurinsa, tana ihu tana cewa, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai! ’Yata tana shan wahala ƙwarai daga aljanin da yake cikinta.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْغَا وَتَ یَرْ ڧَسَرْ كَنْعَنَ تَذُواْ تَطَغَ مُرْيَ تَثٜىٰ «كَيِ مِنِ جِنْڧَيْ، يَا عُبَنْ‌غِجِ ، طَنْ دَاوُدَ؞ وَنِ أَلْجَنِ يَنَ بَا یَتَ وَهَلَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ga wata Bakan'aniya mutuniyar ƙasar, ta zo, ta ɗaga murya ta ce, “Ya Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayina. Wani aljani ya bugi 'yata, ba yadda take.”