Matthew 17:20 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya amsa ya ce, “Saboda kuna da ƙarancin bangaskiya sosai. Gaskiya nake gaya muku, in kuna da bangaskiyar da take ƙanƙanuwa kamar ƙwayar mustad, za ku iya ce wa wannan dutse, ‘Matsa daga nan zuwa can,’ zai kuwa matsa. Babu abin da zai gagare ku.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عِيسَىٰ يَثٜىٰ مُسُ «سَبُواْدَ بَنْ‌غَسْكِيَرْكُ ڧَرَمَ ثٜىٰ؞ حَڧِيڧَ إِنَ غَيَ مُكُ، عِدَنْ كُنَدَ بَنْ‌غَسْكِيَرْ دَ تَيِ ڧَنْڧَنْتَ كَمَرْ ڨُويَرْ مَسْتَدْ، ذَاكُ عِيَثٜىٰ وَتُدُنَّنْ يَتَاشِ دَغَ نَنْ ذُوَا ثَنْ، كُمَ ذَيْ تَاشِ؞ بَ كُوَ أَبِنْدَ ذَيْ غَغَرٜىٰكُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya ce musu, “Saboda ƙarancin bangaskiyarku. Domin hakika ina gaya muku, da kuna da bangaskiya, ko misalin ƙwayar mustad, da za ku ce wa dutsen nan, ‘Kawu daga nan, ka koma can!’, sai kuwa ya kawu. Ba kuwa abin da zai gagare ku. [