Matthew 18:13 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
In kuwa ya same ta, ina gaya muku gaskiya, zai yi murna saboda ɗayan fiye da tasa’in da taran da ba su ɓace ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كُمَ عِدَنْ يَاسَامٜىٰتَ، غَسْكِيَ إِنَ ڢَطَا مُكُ، مُرْنَرْ دَ يَكٜىٰيِ عَكَنْتَ، تَاڢِ تَثَسَعِنْ دَ تَرَنْ دَ بَسُ ٻَتَبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
In kuwa ya samo ta, labudda, ina gaya muku, ai, farin cikin da yake yi a kanta ya fi na tasa'in da taran nan da ba su taɓa ɓăcewa ba.