Matthew 18:21 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Bitrus ya zo wurin Yesu ya yi masa tambaya ya ce, “Ubangiji, sau nawa zan yafe wa ɗan’uwana sa’ad da ya yi mini zunubi? Har sau bakwai?”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَنَانً سَيْ بِتْرُسْ يَذُواْ يَثٜىٰ وَ عِيسَىٰ عُبَنْ‌غِجِ ، سَوْ نَوَ طَنْعُوَنَ ذَيْ يِمِنِ لَيْڢِے إِنْ يَاڢٜىٰمَسَ؟ سَوْ بَݣَويْ؟
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Bitrus ya matso ya ce masa, “Ya Ubangiji, sau nawa ɗan'uwana zai yi mini laifi in yafe masa? Har sau bakwai?”