Matthew 19:12 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Gama waɗansu bābānni ne domin haka aka haife su; waɗansu kuwa mutane ne suka mai da su haka; waɗansu kuma sun ƙi aure ne saboda mulkin sama. Duk mai iya ɗaukar wannan yă ɗauka.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَݣَويْ وَطَنْدَ عَكَ حَيْڢَ دَ بَذَاسُ عِيَيِنْ عَوْرٜىٰبَ؞ أَݣَويْ وَطَنْدَ مُتَنٜىٰنٜىٰ سُكَ مَيْدَسُو حَكَ؞ أَݣَويْ كُمَ وَطَنْدَ سُكَ يَرْدَ بَذَاسُيِ عَوْرٜىٰبَ دُواْمِنْ ڧَوْنَرْ مُلْكٍ سَمَ؞ دُكْ مَيْ عِيَ طَوْكَرْ مَغَنَرْ نَنْ يَطَوْكَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Akwai waɗanda aka haifa babanni, akwai waɗanda mutane ne suka mai da su babanni. Akwai kuma waɗanda suka mai da kansu babanni domin ƙaunar Mulkin Sama. Duk mai iya ɗaukar maganar nan, yă ɗauka.”