Matthew 2:13 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Bayan sun tafi, sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusuf a mafarki ya ce, “Tashi, ka ɗauki yaron da mahaifiyarsa, ku gudu zuwa Masar. Ku zauna a can sai na gaya muku, gama Hiridus zai nemi yaron don yă kashe.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَايَنْدَ سُكَ تَڢِے سَيْ وَنِ مَلاَىِٕكَنْ عُبَنْغِجِ يَبَيَّنَ وَ يُوسُڢَ أَمَڢَرْكِ، يَثٜىٰ، «تَاشِ، كَطَوْكِ طَنْ يَرُواْنَّنْ دَ مَامَرْسَ كُغُدُ ذُوَا ڧَسَرْ مَصَرْ؞ كُذَوْنَ عَثَنْ سَيْ نَڢَطَا مُكُ كُدَاوُاْ، غَمَا هِرُدُسْ ذَيْ نٜىٰمِ طَنْ يَرُوانْ دُواْمِنْ يَكَشٜىٰشِ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da suka tashi, sai ga wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki, ya ce, “Tashi ka ɗauki ɗan yaron da mahaifiyarsa, ka gudu ƙasar Masar, ka zauna a can sai na faɗa maka, don Hirudus yana shirin binciko ɗan yaron yă hallaka shi.”