Matthew 2:22 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma da ya ji Arkelawus ne yake mulki a Yahudiya a matsayin wanda ya gāji mahaifinsa Hiridus, sai ya ji tsoron zuwa can. Bayan an gargaɗe shi a mafarki, sai ya ratse zuwa gundumar Galili,
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا دَ يَجِ طَنْ هِرُدُسْ، وَتُواْ أَرْكِلَيُسْ يَا ثِغَادُوانْ بَابَنْسَ، يَنَ مُلْكٍ يَنْكِنْ يَهُودِيَ، سَيْ يَجِڟُواْرُواْ يَتَڢِے ثَنْ؞ عَمَّا دَ عَكَ جَا مَسَ كُنّٜىٰ أَمَڢَرْكِ، سَيْ يَرَڟٜىٰ ذُوَا يَنْكِنْ غَلِيلِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma da ya ji Arkilayus ya gāji ubansa Hirudus, yana mulkin ƙasar Yahudiya, sai ya ji tsoron isa can. Amma da aka yi masa gargaɗi a mafarki, sai ya ratse zuwa ƙasar Galili.