Matthew 21:23 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Yesu ya shiga filin haikali, yayinda yake koyarwa, sai manyan firistoci da dattawan mutane suka zo wurinsa suka yi tambaya, “Da wane iko kake yin waɗannan abubuwa? Kuma wa ya ba ka wannan iko?”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ عِيسَىٰ يَشِغَ هَيْكَلِ، يَنَ ثِكِنْ كُواْيَرْوَا كٜىٰنَنْ، سَيْ مَنْيَنْ ڢِرِسْتُواْثِے دَ شُوغَبَنِّنْ جَمَعَ سُكَذُواْ وُرِنْسَ سُكَثٜىٰ «دَ وَنٜىٰ إِظْنِ كَكٜىٰيِنْ أَبُبُوَنَّنْ، كُمَ وَيَبَاكَ وَنَّنْ إِظْنِ؟»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya shiga Haikali yana cikin koyarwa, sai manyan firistoci da shugabannin jama'a suka zo wurinsa, suka ce, “Da wane izini kake yin abubuwan nan, wa ya ba ka izinin?”