Matthew 21:33 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Ku saurari wani misali. An yi wani mai gona wanda ya yi gonar inabi. Ya kewaye ta da katanga, ya haƙa wurin matsin inabi a ciki, ya kuma gina hasumiyar gadi. Sa’an nan ya ba wa waɗansu manoma hayar gonar inabin, ya kuma yi tafiya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«تُواْ، غَ وَنِ مِصَالِ كُمَ؞ أَݣَويْ وَنِ مُتُمِنْ دَ يَيِ غُواْنَرْ إِنَبِے، يَكٜىٰوَيٜىٰتَ دَ كَتَنْ‌غَ، يَحَڧَ وُرِنْ مَڟٜىٰوَرْ یَیَنْ إِنَبِے عَثِكِ، يَكُمَ غِنَا رُمْڢَرْ مَيْغَادِ؞ يَبَا وَطَنْسُ مَنُواْمَ هَيَرْ غُواْنَرْ، سَعَنً يَتَڢِے وَتَ ڧَسَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“To, ga kuma wani misali. An yi wani maigida da ya yi garkar inabi, ya shinge ta, ya haƙa ramin matse inabi a ciki, ya kuma gina wata 'yar hasumiyar tsaro. Ya ba waɗansu manoma sufurin garkar, sa'an nan ya tafi wata ƙasa.