Matthew 21:41 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Suka amsa suka ce, “Zai yi wa banzan mutanen nan mugun kisa, yă ba da hayar gonar inabin ga waɗansu ’yan haya, waɗanda za su ba shi rabonsa na amfanin gona a lokacin girbi.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ سُكَثٜىٰ مَسَ «أَيْ، لَلَّيْ ذَيْ كَكَّشٜىٰ مُوغَيٜىٰنَّنْ، يَبَا وَطَنْسُ هَيَرْ غُواْنَرْ، وَطَنْدَ ذَاسُدِنْ‌غَ بَاشِ نَاسَ رَبُوانْ أَمْڢَانِنْ غُواْنَرْ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai suka ce masa, “Zai yi wa mutanen banzan nan mugun kisa, ya ba waɗansu manoma sufurinta, waɗanda za su riƙa ba shi gallar garkar a lokacin nunanta.”