Matthew 21:42 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yesu ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karanta a cikin Nassi cewa, “ ‘Dutsen da magina suka ƙi shi ne ya zama dutsen kusurwar gini. Ubangiji ne ya aikata wannan, kuma abin mamaki ne a idanunmu’?
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عِيسَىٰ يَثٜىٰ مُسُ «أَشٜىٰ، بَكُ تَٻَ كَرَنْتَاوَا أَ رُبُوتَثِّيَرْ مَغَنَرْ اللَّهْ بَ؟ ثٜىٰوَ، « ‹دُوڟٜىٰنْ دَ مَاسُ غِنِ سُكَڧِ، شِينٜىٰ يَذَمَ دُوڟٜىٰ مَڢِے أَمْڢَانِ أَغِنِ؞ وَنَّنْ عَيْكِنْ عُبَنْ‌غِجِ نٜىٰ، أَبِنْ مَامَاكِ نٜىٰ كُوَ أَعِدَنُونْمُ؞› »
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yesu ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karantawa a Littattafai ba? cewa, ‘Dutsen da magina suka ƙi, Shi ne ya zama mafificin dutsen gini. Wannan aikin Ubangiji ne, A gare mu kuwa abin al'ajabi ne.’