Matthew 23:27 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kuna kama da kaburburan da aka shafa musu farin fenti, waɗanda suna da kyan gani a waje, amma a ciki, cike suke da ƙasusuwan matattu da kuma kowane irin abu mai ƙazanta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«كَيْتُوانْكُ، مَلَمً كُواْيَرْوَرْ مُوسَٰى دَ ڢَرِسِيَاوَا، مُنَاڢُكَيْ! كُنَ كَمَرْ كَبُرْبُرَنْ دَ عَكَ شَاڢَ مُسُ ڢَضٍ ڢٜىٰنْتِ، مَاسُ ݣَنْ غَنِ دَغَ وَجٜىٰ، عَمَّا عَثِكِ سَيْ ڧَسُسُوَنْ مَتَتُّو دَ دَتِّ إِرِ إِرِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kamar kaburburan da aka shafa wa farar ƙasa kuke, masu kyan gani daga waje, daga ciki kuwa sai ƙasusuwan matattu da ƙazanta iri iri.