Matthew 26:75 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Bitrus ya tuna da maganar da Yesu ya yi cewa, “Kafin zakara yă yi cara, za ka yi mūsun sani na sau uku.” Sai ya fita waje, ya yi ta kuka.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ بِتْرُسْ يَتُنَ دَ مَغَنَرْ دَ عِيسَىٰ يَيِ مَسَ ثٜىٰوَ «كَاڢِنْ ظَكَرَ يَيِ ثَارَ، ذَاكَيِ مُسُونْ سَنِنَ سَوْ عُكُ؞» سَيْ بِتْرُسْ يَڢِتَ وَجٜىٰ يَيِ كُوكَا مَيْذَاڢِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Bitrus ya tuna da maganar Yesu cewa, “Kafin carar zakara za ka yi musun sanina sau uku.” Sai ya fita waje, ya yi ta rusa kuka.