Matthew 27:3 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da Yahuda, wanda ya bashe Yesu, ya ga an yanke wa Yesu hukuncin kisa, sai ya yi “da na sani.” Ya je mayar wa manyan firistoci da dattawan kuɗin azurfa talatin ɗin.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ يَهُودَ وَنْدَ يَبَاشٜىٰشِ يَغَ أَنْيَنْكٜىٰوَ عِيسَىٰ حُكُنْثِنْ مُتُوَ، سَيْ يَيِ بَڧِنْ ثِكِ، يَدَاوُاْ وُرِنْ مَنْيَنْ ڢِرِسْتُواْثِے دَ شُوغَبَنِّ، يَمَيَرْ مُسُ دَ كُطِنْ أَظُرْڢَا تَلَاتِنْ طِنَّنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da Yahuza mai bashe shi ya ga an yanke masa hukuncin kisa, sai ya yi nadama, ya mayar wa manyan firistoci da shugabanni da kuɗi azurfa talatin ɗin nan,