Matthew 27:40 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
suna cewa, “Kai da za ka rushe haikali, ka kuma gina shi cikin kwana uku, ceci kanka mana! In kai Ɗan Allah ne, ka sauka daga gicciyen!”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سُنَ ثٜىٰوَ «كَيْ دَ كَاثٜىٰ ذَاكَ رُشٜىٰ هَيْكَلِ، كَكُمَ غِنَا شِ ثِكِنْ ݣُونَ عُكُ، كَثٜىٰثِ كَنْكَ مَنَ! عِدَنْ كَيْ طَنْ اللَّهْ نٜىٰ، كَسَوْكُواْ دَغَ غِثِّيٜىٰنْ مَنَ!»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
suna cewa, “Kai da za ka rushe Haikalin, ka kuma gina shi a cikin kwana uku, ceci kanka mana! In kai Ɗan Allah ne, to sauko daga gicciyen mana!”