Matthew 27:60 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan ya sa shi a sabon kabarinsa, wanda ya haƙa a dutse. Bayan ya gungura wani babban dutse ya rufe bakin kabarin, sai ya tafi abinsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَسَاشِ عَثِكِنْ سَابُوانْ كَبَرِ نَاسَ، وَنْدَ يَحَڧَ أَجِكِنْ دُوڟٜىٰ؞ سَيْ يَتُورَ بَبَّنْ دُوڟٜىٰ عَبَڧِنْ كَبَرِنْ، يَتَڢِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
ya sa shi a wani sabon kabari da ya tanadar wa kansa, wanda ya fafe a jikin dutse. Sai ya mirgina wani babban dutse a bakin kabarin, ya tafi.