Matthew 27:64 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka, ka ba da umarni, a tsare kabarin sai rana ta uku ɗin. In ba haka ba, almajiransa za su iya zuwa su sace jikin, sa’an nan su faɗa wa mutane cewa, an tashe shi daga matattu. Ruɗin ƙarshen nan fa, sai yă fi na farkon muni.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَبُواْدَ حَكَ كَسَا عَيِ غَادِنْ كَبَرِنَّنْ سُواْسَيْ حَرْ ذُوَا رَانَ تَ عُكُ، دُواْمِنْ كَدَ أَلْمَجِرَنْسَ سُتَڢِے سُسَاثِ غَاوَرْسَ، سَعَنً سُثٜىٰ وَمُتَنٜىٰ يَتَاشِ دَغَ مَتَتُّو؞ رُوطِنْ ڧَرْشٜىٰ ڢَا ذَيْڢِ نَڢَرْكُوانْ مُونِ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Saboda haka sai ka yi umarni a tsare kabarin nan sosai har rana ta uku, kada almajiransa su sace shi, sa'an nan su ce wa mutane wai ya tashi daga matattu. Yaudarar ƙarshe za ta fi ta farkon muni ke nan.”