Matthew 28:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kwaram, sai ga Yesu ya gamu da su ya ce, “Gaisuwa.” Sai suka zo kusa da shi, suka rungumi ƙafafunsa, suka yi masa sujada.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ عِيسَىٰ دَ كَنْسَ يَسَدُ دَسُو، يَثٜىٰ مُسُ «سَلَّمَرْكُ دَيْ!» سُكَ مَڟُواْ كُسَ سُكَ ضُنْغُمٜىٰ ڧَڢَاڢُنْسَ، سُكَيِ مَسَ سُجَّدَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai kuwa ga Yesu ya tarye su, ya ce, “Salama alaikun!” Suka matso suka rungume ƙafafunsa, suka yi masa sujada.