Matthew 5:15 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Mutane ba sa ƙuna fitila su rufe ta da murfi. A maimako, sukan ajiye ta a kan wurin ajiye fitila, takan kuma ba da haske ga kowa a cikin gida.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَعَكُنَّ ڢِتِلَ أَ رُڢٜىٰتَ دَ ݣُونُواْ، سَيْدَيْ عَ أَجِيٜىٰتَ عَكَنْ سَنْدَا مَيْ رِڧٜىٰ ڢِتِلُ عِنْدَ ذَاتَ بَادَ حَصْكٜىٰ غَ دُكَنْ مُتَنٜىٰنْ غِدَنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ba a kunna fitila a rufe ta da masaki, sai dai a ɗora ta a kan maɗorinta, sa'an nan ta ba duk mutanen gida haske.