Matthew 5:22 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma ina gaya muku, duk wanda ya yi fushi da ɗan’uwansa, za a hukunta shi. Kuma duk wanda ya ce wa ɗan’uwansa ‘ Raka,’ za a kai shi gaban Majalisa. Amma duk wanda ya ce, ‘Kai wawa!’ Zai kasance a hatsarin shiga jahannama ta wuta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا إِنَ غَيَ مُكُ، وَنْدَ يَكٜىٰ ڢُشِے دَ طَنْعُوَنْسَ، ذَاعَ حُكُنْتَشِ؞ وَنْدَ يَكِرَا طَنْعُوَنْسَ بَنْظَ، ذَاعَ كَيْشِ كُواْتُ؞ وَنْدَ كُمَ يَكِرَا طَنْعُوَنْسَ وَاوَا، يَا دَاثٜىٰ دَ غِدَنْ وُتَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma ni ina gaya muku, kowa yake fushi da ɗan'uwansa ma, za a hukunta shi. Kowa ya ce da ɗan'uwansa wawa, za a kai shi gaban majalisa. Kowa kuma ya ce, ‘Kai wofi!’ hakkinsa shiga Gidan Wuta.