Matthew 5:30 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
In kuma hannunka na dama yana sa ka yin zunubi, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikinka, da a jefa jikinka ɗungum a cikin jahannama ta wuta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عِدَنْ حَنُّنْكَ نَدَمَ يَنَ سَاكَ كَيِ ذُنُوبِ، كَثِرٜىٰشِ كَيَرْ؞ غَارَ كَرَسَ وَتَ غَٻَ تَجِكِنْكَ دَ أَ جٜىٰڢَ جِكِنْكَ طُنْغُمْ عَثِكِنْ غِدَنْ وُتَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
In kuma hannunka na dama, yana sa ka yi laifi, to, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓinka da a jefa jikinka ɗungum a Gidan Wuta.”