Matthew 8:26 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya amsa ya ce, “Ku masu ƙarancin bangaskiya, me ya sa kuke tsoro haka?” Sa’an nan ya tashi ya tsawata wa iskar da kuma raƙuman ruwan, sai wuri ya yi tsit gaba ɗaya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ يَثٜىٰ مُسُ «دُوانْمٜىٰ كُكَجِڟُواْرُواْ حَكَ، يَا كُو مَاسُ ڧَرَمَرْ بَنْغَسْكِيَ؟» سَيْ يَتَاشِ يَڟَاوَتَاوَ إِسْكَرْ دَ كُمَ تٜىٰكُنْ، سَيْ وُرِنْ دُكْ يَيِ ڟِتْ!
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya ce musu, “Don me kuka firgita haka, ya ku masu ƙarancin bangaskiya?” Sa'an nan ya tashi, ya tsawata wa iskar da ruwan. Sai wurin duk ya yi tsit!