Micah 2:12 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Tabbatacce zan tattara ku duka, ya gidan Yaƙub; zan tattara ku raguwar Isra’ila. Zan kawo su wuri ɗaya kamar tumaki a cikin garke, kamar garke a wajen kiwonsa; wurin zai cika da mutane.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«حَڧِيڧَ ذَنْ تَتَّرَاكُ يَا ذُرِيَرْ يَعْڧُوبَ، ذَنْ تَتَّارَ ضَغُواْوَرْ جَمَعَرْ إِسْرَٰٓءِيلَ؞ ذَنْ حَطَكُ تَرٜىٰ كَمَرْ غَرْكٜىٰنْ تُمَكِ، كَمَرْ غَرْكٜىٰنْ تُمَكِ أَوُرِنْ كِيوُاْ، ذَاكُ ذَمَ بَبَّنْ تَارُوانْ جَمَعَ وَدَّ ذَاعَ جِ سُورُوتُنْسُ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Hakika zan tattara ku duka, ya Yakubu, Zan tattara ringin Isra'ila. Zan haɗa su tare kamar tumaki a garke, Kamar garken tumaki a makiyaya Za su zama taron jama'a mai hayaniya.