Micah 2:8 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ba da daɗewa ba mutanena sun tashi kamar magabci. Kun tuɓe riga mai tsada daga waɗanda suke wucewa ba tare da kun damu ba, sai ka ce mutanen da suke komowa daga yaƙi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَهْوٜىٰهْ يَأَمْسَ يَثٜىٰ، «عَمَّا كُكَنْيِ دَ مُتَنٜىٰنَ كَمَرْ سُو أَبُواْكَنْ غَابَنٜىٰ؞ كُكَنْ تُوٻٜىٰ رِيغُنَنْ مَاسُ وُثٜىٰوَ ثِكِنْ سَلَمَ، مَاسُ وُثٜىٰوَ بَ دَ تُنَانِنْ يَاڧِبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji ya amsa ya ce, “Ba da daɗewa ba mutanena sun tashi kamar maƙiyi, Kukan tuɓe rigar masu wucewa da salama, masu komawa da yaƙi.