Micah 6:7 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ubangiji zai ji daɗin hadayar raguna dubbai da kuma rafuffukan mai dubbai goma? Zan ba da ɗan farina ne don laifina, ko ’ya’yan jikina domin zunubin raina?
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كُواْ رَغُنَ دُبَّيْنٜىٰ ذَاسُ غَمْشِ يَهْوٜىٰهْ ؟ كُواْ كُواْغُنَ دُبُنْ دُبَّيْ نَمَنْ ظَيْتُنّٜىٰ؟ كُواْ إِنْ بَادَ طَنْ ڢَارِنَ دُواْمِنْ هَدَايَرْ لَيْڢُواْڢِنَ نَسَاٻُواْ؟ كُواْ إِنْ بَادَ یَیَنَ دُواْمِنْ ذُنُبَيْنَ؟»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji zai yi murna da raguna dubbai Ko kuwa da kogunan mai dubbai? Zan ba da ɗan farina ne don laifina? Ko kuwa zan ba da 'ya'yana saboda zunubina?