Nahum 2:12 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zaki ya kashe abin da ya ishe ’ya’yansa ya kuma murɗe wuyan dabbobi ya cika wurin zamansa da abin da ya kama ya cika kogwanninsa da abin da ya kashe.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَاكِ يَيَيَّاغٜىٰ أَبِنْ دَ يَ إِشٜىٰشِ دَ یَیَنْسَ، يَكُمَ كَشٜىٰ وَ ظَكَنْيَرْسَ دَبَّ؞ يَثِكَ كُواْغُوانْسَ دَ غَنِمَ، كُواْڠُونِّنْسَ كُمَ دَ نَمُواْمِنْ دَاجِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Zaki ya kashe abin da ya ishi kwiyakwiyansa. Ya kaso wa zakanyarsa abin da ya ishe ta. Ya cika kogonsa da ganima.