Nahum 3:10 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Duk da haka an tafi da ita ta kuma tafi bauta. Aka fyaɗa ƙanananta da ƙasa aka yayyanka su gunduwa-gunduwa a kan kowane titi. Aka jefa ƙuri’a a kan manyan mutanenta, aka daure manyan mutanenta da sarƙoƙi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكْ دَ ڧَرْڢِنْتَ أَنْ كَيْتَ بَوْتَا أَنْتَڢِے دَ عِتَ ذُوَا بَڧُوَرْ ڧَسَا؞ أَنْ ڢَرْڢَشٜىٰ كَوُنَنْ یَنْ يَارَنْتَ، عَكَنْ كُواْوَنٜىٰ ݣُونَ تَتِيتِ؞ أَنْ رَرَّبَ دَتَّاوَنْتَ تَوُرِنْ جٜىٰڢَ ڧُرِعَ، أَنْطَوْرَ دُكَنْ مَنْيَنْ مُتَنٜىٰنْتَ دَ سَرْڧَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Duk da haka an tafi da ita, an kai ta cikin bauta. An fyaɗa ƙanananta a ƙasa, An yi kacakaca da su a kowace mararraba. An jefa kuri'a a kan manyan mutanenta, Aka ɗaure dukan manyan mutanenta da sarƙoƙi.