Nahum 3:17 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Masu tsaronki suna kama da fāri ɗango, shugabanninki sun yi cincirindo kamar fārin ɗango da suka sauka a kan bango a rana mai sanyi, amma da rana ta fito, duk za su tashi su tafi, ba kuma wanda ya san inda suka nufa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مَاسُ غَادِنْكِ كَمَرْ ڧُدَنْ ظُمَ مَاسُ وُثٜىٰوَ سُكٜىٰ، دَتَّاوَنْكِ كَمَرْ ڢَارِنٜىٰ، سُنَ ظَوْنٜىٰ عَكَنْ ثِيَوَ أَ لُواْكَثِنْ سَنْيِ؞ دَ ذَاڢِنْ رَانَ يَڢِتَ، سَيْ سُتَاشِ، بَاوَنْدَ يَسَنْ عِنْدَ سُكَ تَڢِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Shugabanninki kamar ɗango suke, Manyan mutanenki kamar cincirindon fāra ne, Suna zaune a kan shinge a kwanakin sanyi, Sa'ad da rana ta fito, sukan tashi su tafi, Ba wanda ya san inda suke.