Nehemiah 12:22 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Shugabannin iyalin Lawiyawa a kwanakin Eliyashib, Yohiyada, Yohanan da Yadduwa, da kuma na firistoci, an rubuta su a zamanin mulkin Dariyus mutumin Farisa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَ لُواْكَثِنْ دَ دَرِيُسْ يَكٜىٰ مُلْكٍ ڢَٰشِيَ نٜىٰ، عَكَ رُبُوتَ سُونَيٜىٰنْ شُوغَبَنِّنْ غِدَنْ كَاكَنِّنْ لَوِيَاوَا دَ نَڢِرِسْتُواْثِے نَظَامَانِنْ عٜىٰلِيَشِبْ دَ يُواْيِيَدَ دَ يُواْهَنَنْ دَ كُمَ يَدُّوَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A zamanin Eliyashib, da Yoyada, da Yohenan, da Yadduwa, Lawiyawa, har zuwa zamanin mulkin Dariyus, mutumin Farisa, aka rubuta shugabannin gidajen kakannin Lawiyawa da firistoci.