Nehemiah 12:24 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Shugabannin Lawiyawa kuwa su ne Hashabiya, Sherebiya, Yeshuwa ɗan Kadmiyel, da ’yan’uwansu, waɗanda suka tsaya ɗaura da su don su yi yabo da kuma godiya, sashe ɗaya kan ba da amsa ga ɗaya sashen, kamar yadda Dawuda mutumin Allah ya umarta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَا سُونَيٜىٰنْ شُوغَبَنِّنْ عِيَلَنْ لَوِيَاوَا؞ هَشَبِيَ دَ شٜىٰرٜىٰبِيَ دَ يٜىٰشُوَ، طَنْ كَدْمِيٜىٰلْ؞ یَنْعُوَنْسُ سُكَنْ ڟَيَ عِنْدَ ذَاسُ ڢُسْكَنْثِ جُونَ دُواْمِنْ سُرٜىٰرَ وَاڧُواْڧِنْ يَبُواْ دَ نَغُواْدِيَ، سَاشٜىٰ طَيَ يَنَ طَوْكَرْ وَاڧَا، سَاشٜىٰ طَيَ يَنَ أَمْسَاوَا، بِسَغَ عُمَرْنِنْ دَ دَاوُدَ مُتُمِنْ اللَّهْ يَبَايَرْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Shugabannin Lawiyawa kuwa, su ne Hashabiya, da Sherebiya, da Yeshuwa, da Kadmiyel. 'Yan'uwansu suna tsaye kusa da su daki daki domin su yi yabo, su yi godiya kamar yadda Dawuda mutumin Allah ya umarta.