Nehemiah 12:36 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
da ’yan’uwansa, Shemahiya, Azarel, Milalai, Gilalai, Ma’ai, Netanel, Yahuda da Hanani, tare da kayan kiɗi da Dawuda mutumin Allah ya umarta. Ezra malamin Doka ya jagoranci jerin gwanon.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَثِكِنْ یَنْعُوَنْ زَكَرِيَّا وَطَنْدَ سُكَبِيسُ أَݣَويْ شٜىٰمَيَ دَ أَظَرٜىٰلْ دَ مِلَلَيْ دَ غِلَلَيْ دَ مَعَيْ دَ نٜىٰتَنٜىٰلْ دَ يَهُودَ دَ كُمَ هَنَنِ؞ دُكَنْسُ كُوَ سُنَ رِڧٜىٰ دَ كَايَنْ كَطٜىٰ كَطٜىٰ إِرِنَّ سَرْكِے دَاوُدَ، مُتُمِنْ اللَّهْ ؞ عُزَيْرُ مَلَمِنْ كُواْيَرْوَرْ مُوسَٰى كُوَ يَنَ مُسُ جَغُواْرَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sauran 'yan'uwansa su ne Shemaiya, da Azarel, da Milalai, da Gilalai, da Ma'ai, da Netanel, da Yahuza, da Hanani. Suna da kayayyakin bushe-bushe da na kaɗekaɗe. Ezra magatakarda ne yake gabansu.