Nehemiah 12:44 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A lokacin an naɗa mutane su lura da ɗakunan ajiya don sadakoki, nunan fari da kuma zakka. Daga gonakin garuruwan da suke kewaye za su kawo sassan da Dokar ta umarta zuwa ɗakunan ajiya domin firistoci da Lawiyawa, gama Yahuda ya ji daɗin aikin firistoci da Lawiyawa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَ لُواْكَثِنْ كُوَ عَكَسَا مُتَنٜىٰنْ دَ ذَاسُلُورَ دَ طَكُنَنْ أَجِيَ، وُرِنْ دَ عَكَنْ أَجِيٜىٰ بَايَرْوَ دَ نُونً ڢَارِ نَأَمْڢَانِنْ غُواْنَ دَ كُمَ زَكَّ تَكَايَنْ دَ عَكٜىٰ كَٰوُاْوَ؞ مُتَنٜىٰنْ ذَاسُدِنْغَ تَارَ رَبُوانْ أَمْڢَانِنْ غُواْنَ دَغَ غُواْنَكِنْ دَسُكٜىٰ كٜىٰوَيٜىٰ دَ غَرُرُوَ دُواْمِنْ ڢِرِسْتُواْثِے دَ لَوِيَاوَا، كَمَرْ يَدَّ كُواْيَرْوَرْ مُوسَٰى تَعُمَرْتَ؞ مُتَنٜىٰنْ يَهُودَ سُكَ دِنْغَ يِنْ حَكَ غَمَا سُنْ جِ دَاطِنْ ڢِرِسْتُواْثِے دَ لَوِيَاوَا وَطَنْدَ سُكٜىٰيِنْ حِدِمَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A ran nan aka sa mutanen da za su lura da ɗakunan ajiya, da sadakoki, da nunan fari, da zaka. Su ne za su tara nunan fari daga gonakin da suke kusa da garuruwa, bisa ga yadda doka ta ce, saboda firistoci da Lawiyawa, gama mutanen Yahuza sun yi murna saboda hidimar da firistoci da Lawiyawa suka yi.