Nehemiah 12:45 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sun yi hidimar Allahnsu da kuma hidimar tsarkakewa, kamar yadda mawaƙa da matsaran ƙofofi suka yi, bisa ga umarnin Dawuda da ɗansa Solomon.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ڢِرِسْتُواْثِے دَ لَوِيَاوَا سُكَ كِيَايٜىٰ ڧَٰعِدُواْدِنْ سُجَّدَ غَ اللَّهْ نْسُ دَ ڧَٰعِدُواْدِنْ ڟَبْتَثٜىٰوَ بِسَغَ عُمَرْنِنْ سَرْكِے دَاوُدَ دَ طَنْسَ سُلَيْمَٰنُ؞ حَكَ مَا مَوَاڧَ دَ مَاسُ غَادِنْ ڧُواْڢُواْڢِنْ هَيْكَلِ سُكَيِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sun yi wa Allahnsu sujada, sun yi hidimar tsarkakewa tare da mawaƙa da masu tsaron ƙofofi kamar yadda Dawuda da ɗansa Sulemanu suka umarta.